‘Yar Arewa, A’isha Abubakar daga jihar Nasarawa, ta shiga gasar cin Sarauniyar kyau ta Najeriya a shekarar 2023.
Saidai a wancan lokacin A’isha ta rika saka kaya masu alamar mutunci amma bata samu lashe gasar ba.

Saidai a shekarar 2025, A’isha ta sake shiga gasar, saidai a wannan karin, ta cire kayan mutuncin inda ta koma saka kaya masu nuna tsiraici.
Saidai a wannan karin ma bata ci gasar ba.

Da yawa sun rika mata Allah kara.
Ana ci gaba da yada Bidiyon A’isha a kafafen sada zumunta.