Friday, December 5
Shadow

Ji zazzafan Martanin Sowore bayan da DSS suka nemi X ta kulle shafinsa

Mawallafin jaridar Sahara reporters, Omoyele Sowore sannan dan fafutuka ya bayyana cewa, X sub aika masa da sako cewa, Gwamnatin Najeriya ta nemi a kulle masa shafi.

Sannan ya goge rubutun da yayi akan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.

Shi dai Sowore ya rubuta cewa “wannan me laifin, Tinubu ya je kasar Brazil ya ce ya magance matsalar rashawa da cin hanci amma hakan ba gaskiya bane”

DSS sun ce wannan bayani na Sowore labarin karyane sannan yana barazana ga tsaron Najeriya hakanan kuma ya batawa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu suna a idon Duniya, dan haka suka nemi X ta kulle shafin Sowore nan da awanni 24 ko kuma a dauki mataki akanta.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Wallahi Aure Nake So Amma Babu Hali Saboda Maraicina" Inji Wannan Baiwar Allah, Ji Labarinta me ban tausai

Saidai Sowore yace ba zai goge wannan rubutu da yayi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *