
Wannan me yin Tiktok din me suna Rukayya tace tambayarta shine an ce Maulidin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ake yi amma kuma gashi sai kaga hotunan Inyas a jikin masu Maulidi me yasa haka?
Sannan ta yi tambayar cewa, me yasa ba za’a yi Maulidi a gida ba sai an tare hanya saboda ta fito zata je shago amma aka tare musu hanya.
Sannan tace me yasa Shehunan Darika ke yafa koren mayafi?