
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya kai ziyara jihar Imo tare sa Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Watau Peter Obi.
Sun je halartar wani taron bita da aka shirya ne a birnin Owerri na jihar ta Imo ranar Asabar.
Saidai sun fuskanci zanga-zanga inda iyamurai da yawa suka taru suka ce El-Rufai ba zai shiga dakin taron ba saboda irin abinda yawa Kiristoci a lokacin da yayi gwamnan jihar Kaduna.
Sun kuma ce Peter Obi ya ci amanarsu kuma sun daina goyon bayansa tunda ya kawo musu makiyinsu jiharsu.
Rahoton yace masu zanga-zangar inyamurai sun rika daga kwalaye masu dauke da rubutun cewa kai ma Peter Obi ka zama makiyin mu kuma mutuncinka ya zube a idonmu saboda kawo mana El-Rufai.
Rahoton yace jami’an tsaro sun so murkushe masu zanga-zangar amma abu ya faskara.
Rahotanni daga kafar Daily Post ya kuma ce dole jami’an tsaro suka samu da kyar suka fitar da El-Rufai daga wajan taron zuwa wani guri dan tsaron lafiyarsa.
Yayin da shi kuma Peter Obi masu zanga-zangar suka ci gaba da yi masa ihun bama so