Friday, December 5
Shadow

Ba zaki dawo majalisa ba>>’Yan majalisar suka sanar da Sanata Natasha Akpoti

Hukumar kula da majalisar tarayya ta ki amincewa da komawar sanata Natasha Akpoti majalisar bayan data kammala dakatarwar watanni 6 da aka mata.

Hukumar tace har yanzu dakatarwar da akawa Sanata Natasha na aiki har sai bayan samun hukuncin kotun daukaka kara.

A baya dai sanata Natasha Akpoti ta kai majalisar kotun tarayya amma majalisar ta yi nasara akanta wanda daga baya ta daukaka kara.

Har yanzu dai maganar na gaban kotun daukaka kara wanda majalisar tace ba zata iya daukar wani mataki akan lamarin ba sai bayan hukuncin kotu.

Karanta Wannan  Fasto Adeboye ya bayyana ranar da zai koma ga Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *