Wani sojan Najeriya ya goge shafinsa na X bayan da aka zargeshi da nuna kiyayya ga musulunci.
Da yawa sun bayyana cewa, Sojan ya rika yin Repost ko kuma yayata kalamai da ake yi na nuna kiyayya ga Musulunci.
Wasu sun rika bayyana cewa, me irin wannan ra’ayi bai kamata a daukeshi aikin tsaron kasa ba.
Da magana ta yi yawa akanshi dai tuni ya goge shafin nasa.