Friday, December 5
Shadow

Ban yadda a bincike ni ba>>Inji Gwamnan Rikon Kwarya na jihar Rivers da shugaba Tinubu ya nada bayan ya kammala wata shida

Gwamnan rikon kwarya na jihar River, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (retd.) Ya bayyana kin amincewa da binciken da majalisar jihar ke son yi masa.

Ya bayyana hakane bayan da majalisar jihar ta amince ta binciki watanni shida da yayi yana matsayin gwamnan jihar.

A ta bakin me magana da yawunsa, Hector Igbikiowubu, Ibas yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya nadashi kuma majalisar tarayya ta rika lura da aikin da yake.

Yace idan dai majalisar tace zata bincikeshi to tana son ta binciki shugaban kasar kenan da majalisar tarayya.

Saidai yace ba bu wanda zai hana majalisar jihar binciken idan tace tana son ta yi.

Karanta Wannan  Kotu ta daure abokai biyu da suka saci kayan sawa tsawon watanni 12 a gidan yari

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *