
Rahotanni sun ce tuni, tsohon Gwamnan jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya fara tetaunawa da shugaban jam’iyyar APC a shirin da yake na komawa jam’iyyar.
Alamun tattaunawar tasu ta bayyana ne jiya, Alhamis, Kamar yanda Jaridar Daily Trust ta bayyana inda tace Kwankwason ya fara tattaunawa da shugaban APC, Prof. Nentawe Yilwatda
Rahoton yace tuni Kwankwaso ya aikawa da hedikwatar Jam’iyyar APC da aniyarsa ta son shiga jam’iyyar a hukumance.
Wata Majiya daga APC ta tabbatarwa da jaridar cewa, Kankwaso da shugaban APC din sun tattauna sosai kuma suna gab da kammala tattaunawar dan shigar Kwankwaso jam’iyyar.