
Tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahya ta shiga cikin sahun wadanda suka mallaki wayar iPhone 17 pro max a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood.
Maryam Yahya ta sanar da mallakar wayar a shafinta na Instagram.
Maryam itace ta 3 bayan Ummi Gayu, da Asiya Chairlady da suka sanar da mallakar wayar a baya.