
Rahotanni daga jihar Kaduna na cewa, An girke jami’an ‘yansanda a duk guraren da aka kafa fastocin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a fadin jihar dan su hana matasa yaga Fastocin.
Wani daga cikin ‘yansandan da aka baiwa aikin tsare fastar shugaban kasar yace an ajiye sune a kan babbar hanyar da shugaba Tinubu zai bi idan ya je Kaduna.
Yace kuma da dare suka fi yin aiki saboda a lokacinne ake sa ran matasa ka iya zuwa su lalata fastocin.
Hakan na zuwane a yayin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai je Kaduna ranar Asabar dan kaddamar da yakin neman zabensa na 2027.