
Malamin Addinin Islama Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana cewa duk da Malam Lawal Triumph yana bangarensu ne amma maganar gaskiya yayi kuskure.
Malam ya bayyana cewa maganar Sheikh Lawal Triumph bata dace da Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba amma kuma bata fitar dashi daga Musulunci ba.
Ya kawo misalin irin hakan data faru a baya inda yace ladabtarwa ce ake wa irin wannan suka yi hakan.
Wannan shine gaskiya idan mutum yayi abu,a fada masa gaskiya