
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, tana nan akan bakanta na cewa, kowa sai ya biya haraji.
Shugaban kwamitin Gyaran fasalin kudi na shugaban kasa, Taiwo Oyedele ne ya bayyana haka a wata ganawa da manema labarai.
Yace a Duniya gaba daya haka tsarin yake, ko ta wace hanya ka samu kudi sai ka biya Haraji, yace idan ance wanda suka samu kudi ta hanyar Halal ne kadai zasu biya haraji, to sai wasu su koma samun kudi ta hanyar Haram dan su kaucewa biyan Harajin.
Yace hukumar karbar Haraji ta kasar Amurka nada taken cewa ko sata kayi sai ka biya Haraji.