
Bankin Duniya wanda shine gaba-gaba wajan baiwa Najeriya bashi yace mutane Miliyan 139 sun tsunduma cikin bakin Talauci a Najeriya.
Bankin yace hakan na zuwane duk da ikirarin da Gwamnatin tarayya ke yi na cewa an samu habakar tattalin arziki.
Bankin yace Gwamnatin sai ta kara himma wajan tabbatar da cewa Talaka na shaida wannan habakar tattalin arzikin da ake cewa an samu idan ana son a ga canji.
Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Varghis ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja wajan taron bayyana ci gaban da aka samu.
Ya jinjinawa Gwamnatin tarayya bisa ga cire tallafin man fetur da daidaita chanjin Naira zuwa kudaden kasashen waje wanda yace hakan matakai ne da zasu zama ginshikai wajan ci gaban Najeriya.
Wannan bayani na bankin Duniya na zuwane kwana daya bayan da Me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya jinjinawa babban bankin Najeriya, CBN kan kokarin da yayi na rage yawan kudin dake zagaye a tsakanin mutane.
Sarkin ya kuma bayyana cewa, tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar ci gaba, bayan da a baya ya kama hanyar Durkushewa.