
Tauraron me wakokin batsa na Arewacin Najeriya, Soja Boy na ci gaba da daukar Bidiyon sabuwar wakar sa wadda yake yi da Iftihal Madaki wadda aka saba gani da Hijabi a baya.
Bidiyon da Soja Boy da Iftihal Madaki ke sakawa a shafukansu na sada zumunta na ci gaba da daukar hankula sosai.
A baya dai Iftihal Madaki ta dauki hankula bayan da aka ganta a wata waka tana rawa da ba’a saba ganin tana yin irinta ba.
Saidai a karo na biyu gashi an sake ganinta a Bidiyon wakar Soja Boy.