Sunday, December 7
Shadow

Yayin da Gwamnatin Tarayya tace Karyace, Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN tace maganar da Amurka ta yi na cewa ana shekye kiristoci da yawa a Najeriya gaskiyane

Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta goyi bayan kasar Amurka da ta ce ana kashe kiristoci a Najeriya da yawa.

Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan ranar Laraba.

Yace kin fadawa kai gaskiya da zargi ba zai kawo karshen matsalar ba

Yace karfin hali da fuskantar matsalar tare ne zai kawo yadda da juna a tsakani.

Yace tabbas Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya musamman yankunan Arewa na fuskantar Kisa da asarar Dukiyoyi da sauransu.

Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ne ya bayyana hakan inda yayi zargin cewa an kashe Kiristoci 52,000 da kona coci-coci 20,000 a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya dai Tuni ta karyata wannan ikirarin na satan kasar Amurkar.

Karanta Wannan  Al'ummar Garin Ringim Dake Jihar Jigawa, Su Ma Sun Bi Sahun Katsinawa Sun Ce 'Ringim Ba Mu Da Korafi'

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *