
Shugaban Najeriya Bola Tnubu zai kama hanyar zuwa Italiya a yau Lahadi domin halartar taron Aqaba na shugabannin ƙasashe kan tsaro.
Fadar shugaban ƙasar ta ce taron Aqaba Process Heads of State and Government Level Meeting zai mayar da hankali kan matsalar tsaro a Afirka ta Yamma.
“Za a fara taron ranar 14 ga watan Oktoba, wanda zai haɗa shugabannin ƙasa, da shugabannin soji daga Afirka domin tattauna ƙalubalen tsaro a Afirka ta Yamma,” in ji sanarwar da fadar ta fitar ranar Asabar da dare.
Sarkin Jordan Abdullah II ne ya ƙaddamar da taron a 2015 domin yaƙi da ta’addanci, wanda Masarautar Jordan da gwamnatin Italiya ke gudanarwa, a cewar sanarwar.
“Shugaba Tinubu zai tattauna da wasu shugabanni a gefen taron domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro a yankin,” kamar yadda fadar ta bayyana.
Ministan Tsaro Badaru Abubakar, da Ƙaramar Ministar Harkokin Waje Bianca Ojukwu, da Mai Ba da Shawara Kan Tsaro Nuhu Ribadu, da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA) Mohammed Mohammed, na cikin jami’an da za su yi wa Tinubu rakiya.