
Bayan Fitowar mahaifin Bilyaminu, watau mijin Maryam Sanda wanda ta kashe yace ya yafewa Maryam Sanda, Asalima Shine ya shiga gaba wajan ganin shugaba Tinubu ya yafewa Maryam din.
Wani dan uwan mamacin ya fito yace Malam Bello Halliru da aka kashe Bilyaminu ya rika damunsu kan maganar gado aka bashi Naira Miliyan 5, amma bai yadda ba, sai da ya kai kotu aka kara masa zuwa Naira Miliyan 10.
Yace amma shine zai fito yana wannan magana.
Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta.
Yafewa Maryam Sanda da shugaba Tinubu yayi ya jawo cece-kuce sosai inda wasu ke ganin hakan bai kamata ba.
