
Wata baiwar Allah ‘yar Najeriya ta gargadi matasan Najeriya da cewa, su daina damuna da sakonnin cewa suna sonta.
Tace bata son Namiji dan Najeriya, Bature take so fari, me fata me laushi wanda zai samar mata da fasfo ya kaita kasarsu.
Ta bayyana hakane a wani Bidiyonta da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta kuma wadannan kalamai nata sun jawo zazzafar Muhawara.