
Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau yace sun ji dadin Abinda Kwamitin Shura na Kano suka yi akan malam Lawal Triumph.
Yace sun jinjina musu, yace amma kuma suna jiran su ga an gayyaci wadanda suka kira Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Raqumi da kuma hankaka, kamar yanda malam Lawal Triumph ya bude littafi ya kawo hujja, suma su bude littafi su kawo Hujjar inda suka ga hakan.
Yace idan kuwa ba a yi hakan ba to ba’awa Ahlussunah Adalci ba.