Wednesday, November 19
Shadow

Akwai yiyuwar Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai fasa yafewa Maryam Sanda bayan da cece-kuce yayi yawa akan yafiyar da aka ma

Rahotanni sun ce akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai canja ra’ayi kan yafiyar da yawa wasu masu laifi dake tsare a gidajen yarin kasarnan.

Yafiyar shugaban kasa ga masu laifi ana yintane dan rage cinkoso a gidajen yari musamman ga masu laifin da ake ganin bashi da tsauri sosai.

Saidai bayan fitowar Jadawalin masu laifin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yafewa an ta cece-kuce musamman saboda ganin wasu sunayen manyan masu laifi da ake ganin bai kamata a yafe musu ba saboda munin laifukan da suka aikata.

Babban lauyan Gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) ya bayyana cewa, har yanzu ba’a kammala yafewa masu laifin ba, ana kan sake dunaba sunayen wadanda akawa yafiyar, inda yace bayan nan ne za’a gabatarwa da hukumar kula da gidajen yarin kasarnan dan a saki wadanda aka yafewa.

Karanta Wannan  Ma'aikatan jinya sun fara yajin aiki a Najeriya

Bayan Maryam Sanda, Kwai wasu masu laifin garkuwa da mutane da aka yafewa da kuma wasu ‘yan fashi da wadanda aka samu da laifin kisan jami’an tsaro wadanda duk jama’a ke ganin bai kamata a yafe musu ba.

Rahoton jaridar Punchng yace akwai yiyuwar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai fasa yafewa manyan masu laifin irin su Maryam Sanda da sauransu saboda suka ta yi yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *