
Shugaban tsaro, Janar Christopher Musa ya baiwa jami’an tsaron sabon Umarni inda yace duk sojan da aka kai daji ba zai rika wuce shekara 2 ba za’a canja masa wajan aiki.
Ya bayyana hakane a yayin da ya kaiwa sojojin ziyara.
Yace kuma duk sojan da aka kai yaki da B0K0 Hàràm ya tabbata ta Kqshe akalla guda daya.
Yace idan aka aika soja daji ya koma bai kashe ko da B0k0 Hàràm guda ba to lallai aikinsa bai cika ba.
Sannan yace sojojin su daina zama suna jiran sai an kawo musu hari su mayar da martani, su rika fita suma suna farautar abokan gaba.