
Gwamnatin tarayya ta kwace gidan Dala Miliyan $2.5 da tsohon ma’aikacin kamfanin mai na kasa, NNPCL, Paulinus Iheanacho Okoronkwo ya siya a kasar Amurka da kudin sata.
A watan Augusta ne aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 30 a gidan yari bayan samunsa da laifin rashawa da cin hanci.
An sameshi da laifin karbar cin hanci har dala Miliyan $2.1 daga wani kamfanin mai me suna Addax Petroleum da zummar cewa zai samarwa da kamfanin lasisin hakar danyen man fetur a Najeriya.
Kuma ya sayi gidanne a Valencia dake California kasar Amurka.