Friday, December 5
Shadow

‘Yansanda sun kama Jarumar Fina-Finan Hausa, Khadija MaiNumfashi an tafi da ita Legas

Rahotanni daga jihar Legas na cewa ‘yansanda sun kama jarumar fina-finan Hausa, Khadija MaiNumfashi.

Rahoton yace kamen da aka mata na da alaka da wani fada da suka yi da kawarta inda kalaman da ta yi akan wani Kabiru legas suka watsu a kafafen sada zumunta.

Rahoton yace Kabiru Legas dinne ya kai korafi wajan ‘yansanda wanda dalilin hakan yasa aka kama jarumar.

Saidai wata kungiyar ‘yan Fim ta nemi a sako Khadija MaiNumfashi saboda a cewarsu, an take hakkinta kuma marainiyace sannan ta shiga harkar fim ta hanyar data dace.

https://www.tiktok.com/@fahadkabirmaitata/video/7565248236512873749?_t=ZS-90qzvNVmMoz&_r=1
https://www.tiktok.com/@aminujtown87/photo/7565156058180652309?_t=ZS-90r2yso25Ev&_r=1
Karanta Wannan  Peter Obi na da masaniya kan ziyarar da na kai wa Abure - Datti

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *