
Rahotanni sun ce dalibai a jami’ar Maradi University dake kasar Nijar sun rushe katangar da aka gina dan raba bangaren maza dana mata a jami’ar.
Hukumomin makarantar sun so raba bangaren maza dana mata a jami’ar amma daliban suka ki amincewa da wannan yunkuri.
Lamarin har sai da ya kai ga Sarkin Maradi ya je makarantar dan ganewa idansa abinda ke faruwa.