Friday, December 5
Shadow

Akwai wadanda lokacin Buhari na kan Mulki sun ta yi masa dadin baki suna ce masa shi mutumin kirki ne amma yana sauka suka fara sukarsa>>Inji Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa, Akwai wadanda suka rika yabon tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari cewa shi mutumin kirki ne kuma babu shugaba Kamarsa a lokacin yana kan mulki.

Yace amma yana sauka daga mulki kuma suka juya suna zaginsa.

Ya bayyana hakane a wajan Taron Tunawa da marigayi Raymond Dokpesi mamallakin tashar talabijin ta AIT da gidan Radion Raypower da kamfanin Daar Communications.

Ya jinjinawa marigayin da kokarin bude gidan Talabijin me zaman kansa na farko a Najeriya.

Karanta Wannan  Wata Sabuwa: Gwagwaren Nijeriya Ku Shirya, Za Mu Fara Karbar Haraji Daga Wajen Ku Domin Rabawa Masu Iyalin Dake Fadin Kasar Nan, Inji Gwamnatin Tarayya, Ta Bakin Ministan Cikin Gida, Olubinmi Tunji-Ojo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *