
Dan majalisar Wakilai, Hon. Abdussamad Dasuki me wakiltar mazabar Kebbe/Tambuwal daga jihar Sokoto ya bayyana cewa ba zai tsaya takara a shekarar 2027 ba.
Yace ya barwa matasa ‘yan kasa da shekaru 40 su tsaya takarar dan kawo sauyi da ci gaba a mazabar tashi.
Yace yayi hakanne ba dan ya gaji ko gazawa ba inda yace har yanzu shi matashi ne amma ya haura shekaru 40.
Yayi godiya ga mutanen mazabatarsa da iyayen gidansa a siyasa da suka bashi dama a shekaru 14 da yayi yana siyasar.