Friday, June 26
Shadow

Dr. Ahmad Gumi ya bukaci gwamnatin Tinubu ta nemi Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya idan kuma yaki janyewa Najeriya ta yanke alakar jakadanci da Amurka

Babban malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bukaci Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta nemi shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya janye barazanar da yawa Najeriya.

Yace shugaba Tinubu ya kira jakadan Amurka ya bukaci kasardu ta janye barazanar da tawa Najeriya.

Sheikh Gumi yace kasa bata fi kasa ba, Najeriya kasa ce me con gashin kanta dan haka bai kamata ta tsaya ana gaya mata abubuwan da basu kamata ba.

Sheikh Gumi yace idan Trump yaki janye kalaman nasa, Najeriya ta yanke huldar jakadancin da Amurkar.

Ya kuma baiwa Gwamnatin shawarar cewa, ta fara neman wasu abokan huldar kasuwanci da sayen makamai bayan Amirka.

Karanta Wannan  Dalibai daga jami'a ta daya a Duniya watau Harvard wadda shuwagabannin kasar Amurka irin su Obama suka yi karatu a cikinta sun zo koyon sanin makamar aiki a matatar man fetur ta Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *