Friday, December 5
Shadow

Hankalin ‘yan Kudu ya tashi sosai suna fadar ashe satar mai zai kawo ku? Bayan da aka bayyana Jihar Rivers a matsayin inda sojojin Amurka zasu sauka idan sun zo Najeriya

Wani bature me suna Dr. Walid Phares ya bayyana cewa, yana bayar da shawara ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya girke sojojin kasar Amurka a Birnin Fatakwal na Jihar Rivers inda yace ta nan ne za’a rika samun damar kai kayan agaji daga Choci-Choci na Duniya.

Saidai wannan magana batawa ‘yab kudu da yawa dadi ba musamman ma ‘yan Jihar ta Rivers inda suke cewa ba yakar matsalar tsaro zata kawo Amurka Najeriya ba, Satar mai ne zai kawo su.

Shugaban kasar Amurka, Donald Trump dai ya bayyana aniyarsa ta son Afkawa Najeriya da hare-hare da sunan yaki da masu yiwa kiristoci Khisan Kyiyashi.

Karanta Wannan  DA ƊUMI-ƊUMI: An Yi Yunƙurin Hallãķa Laftanar Yerima Yau A Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *