
Wasu ‘yan matan Solo sun fito sun zargi Tauraron fina-finan Hausa, Musbahu Anfara da aikata Alfasha.
Sun ce duk macen da ta je gidan solonsa sai yayi Alfasha da ita.
Sun kara da zargin cewa, mata 2 suka sani wadanda ya dirkawa cikin shege.
Hakan ya biyo bayan hirar da Hadiza Gabon ta yi dashine inda ya bayyana cewa yana soyayya da ‘yan Fim amma ba zai iya aurensu ba.
Yace dalilinsa shine yana son matar da zai aura ta zama zata iya hakura dashi kadai.