
Gwamnan jihar Naija, Umar Bago ya jaddada aniyarsa ta cewa, sai malami ya yanki Lasisi a jihar kamin a barshi yayi wa’azi.
Yace ba zasu bari malami ya hau mumbari ya rika zagin gwamnati da duk wanda yaga dama ba ko ya kawo wata sabuwar akida ba.
Yace duk malamin da ya ga hakan bai masa ba, yana iya karawa gaba.