
Rahotanni sun bayyana cewa, an garzaya da Tauraron fina-finan Indiya, Prem Chopra zuwa Asibiti.
Babu dai cikakken bayani kan irin rashin lafiyar dake damunshi.
Hakanan abokin aikinsa, Dram shima yana can kwance a Asibiti inda tuni har an fara yada rade-radin cewa ya mutu amma iyalansa sun musanta hakan.