Friday, December 5
Shadow

Ya kamata ana bin doka a kasarnan, Masu son hadani fhada da sojoji ne suke rura whutar rikicin amma ni ina girmama sojoji kuma banda matsala dasu>>Inji Wike

Ministan babban birnin tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, yana girmama sojoji kuma bashi da matsala dasu.

Ya bayyana hakane a yayin da ake ci gaba da takaddama akan Tirka-Tirkar data faru tsakaninsa da sojan ruwa, AM. Yerima wanda ya hanashi shiga wani fili a Abuja.

Wike yace ya je wajanne bayan samun rahoton cewa, an ciwa daya daga cikin ma’ikatansa Zarafi, yace shi kuma ba zai bari a rika ciwa ma’aikatan dake karkashinsa zarafi ba.

Yace idan an kaika wajan gadi a matsayin jami’in tsaro aka ce ka harbi mutum, idan ka kashye mutum kana tunanin doka ba zata yi aiki akanka bane?

Karanta Wannan  Da ya dauki bìndìgàr mahaifinsa dansanda ya harbe mahaifin ya mùtù

Yace bashi da matsala da sojoji da yasan yana da matsala da sojoji akwai inda zai je ya warware matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *