Thursday, February 5
Shadow

Nima ban amince da kirar da akawa Wike daga PDP ba>>inji Gwamnan jihar Flato>>Caleb Mutfwang

Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana cewa, bai goyi bayan korar da akawa ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam’iyyar PDP ba.

Ya bayyana hakane a sanarwar da ya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Gyang Bere.

Hakan na zuwane bayan da PDP ta sanar da korar Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga cikin jam’iyyar.

Gwamna Mutfwang ya bayyana cewa ba a tattauna wannan masala a taron gwamnonin jam’iyyar ba hakanan ba’a san da ita ba dan haka shi baya goyon bayan korar Wike.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:Ganin Sanata Adams Oshiomhole tare da wata mata me yin irin fina-finan nan na Alfasha ya jawo cece-kuce sosai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *