
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta tabbatar da cewa, dokar hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga a Najeriya dan kariyar kai har yanzu tana aiki.
Me magana da yawun hukumar, Benjamin Hundeyin ne ya bayyana haka a wani martani da yayi game da ikirarin da wani yayi cewa ya mallaki Bindigar AK47.
Benjamin yace a doka ko da ana bada lasisi, Bindigar AK47 bata cikin wadda aka amince farar hula su rike.
Yace amma a yanzu har yanzu ba’a dage dokar data hana bayar da lasisin Mallakar Bindiga dan kariyar kai ba.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda mutane suka rika tambayar to su tsageran daji ina suka samo nasu Bindigun?