
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa hanyar da Gwamnatin yanzu ta dauka itace ta baiwa tsageran Daji kudi da kayan abinci wai dan a rika lallabasu kada su rika kai hare-hare kan al-umma.
Yace jihohi da yawa na Arewa na kan wannan tsarin ciki hadda jihar Kaduna.
Malam ya kara da cewa a jihar Kaduna Naira Biliyan 1 aka baiwa tsageran dajin.
Yace suna da hujjoji akan hakan kuma idan lokaci yayi zasu fitar dasu.
Malam ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.