
Wani Malamin Tsubbu ya buga Qasa yace taurari sun nuna Bayern Munich ce zata ci Arsenal a wasan Champions League da zasu buga anjima.
Ya bayyana hakane a shafinsa na Tiktok bayan da wani ya aika masa sakon bukatar ya duba musu waye zai yi nasara
Malamin Tsubbun yace duk da baya ta’ammuli da harkar kwallo amma wai Taurari sun gaya masa cewa, Bayern Munich ce zata yi nasara.