
Sanata Ali Ndume ya ya nemi Ministan baban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike da ya daina kamawa da korar Almajirai da sauran ‘yan Asalin Abuja dake yawo a tituna.
Yace maimakon korarsu, kamata yayi Ministan Abujan yayi irin abinda Kano ke yi na samar da wani guri na musamman dan a rika koyawa irin wadannan mutanen sana’a.
Saidai Wike yace hakan ba za yiyu ba dan Abuja ta banbanta da duk wata sauran jihar Najeriya.