
Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa a matsayin El-Rufai wanda ya taba yin gwamnan jihar Kadua, kuma ya kai shekaru 65, kamata yayi ya koma gida yana nema gafarar Allah.
Yace tsinuwar da El-Rufai yake yawan yiwa mutane ce ta koma masa gida.
Yace Dama idan ka yi tsinuwa idan bata hau kan wanda ka tsinemawa ba, to zata dawo kanka ne ko kan ‘ya’yanka.