Friday, December 26
Shadow

Dalibai Kiristoci na Jami’o’in Federal University Kashere, Gombe da BUK Kano sun koka da cewa akwai masallatai da yawa a wadannan jami’o’in amma an hanasu gina coci ko guda daya

Daliban jami’o’in Federal University Kashere, Gombe dana jami’ar BUK, Kano Kiristoci sun koka da cewa, akwai masallatai da yawa a wadannan jami’o’in amma an hanasu gina coci ko guda daya.

Daya daga cikin daliban na Kashere ne ya fito yake zanga-zanga shi kadai inda yace suna bukatar Coci a jami’ar.

Wani kirista ta bayyana cewa abin haushin shine jihar Gombe da yawan musulmai da kirista daidai suke watau 50/50 amma irin wannan abin na faruwa.

Karanta Wannan  Maganin ciwon zuciya na Gargajiya

Wannan zanga-zanga da dalibin yayi tasa shima wani dalibin jami’ar BUK Kano ya bayyana cewa suna hakan take, akwai masallatai a BUK amma su ba’a basu damar gina coci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *