Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Mansurah Isah ta bayyana cewa, duk wanda ya zageta saboda ta roki Ahmed Musa kyautar Naira Miliyan 10 bata yafe ba.
Tace hakanan duk wanda suka zageta saboda zawarci tafa fatan Allah yasa ‘ya’yansu ko wasu mata na jikinsu su yi dan su ji zafin abin su tuba.

