
Tauraruwar fina-finan Hausa, Hadiza Gabon ta saki sabon Bidiyon dan baiwa Magoya bayan Adam A. Zango dake sukarta Haushi.
Ta saki Bidiyo ne a Tiktok inda ta dora wakar Gambara da Dapboy ne suna Lokaci.
Fada tsakanin Magoya bayan Adam A. Zango da Hadiza Gabon ya samo Asali ne bayan da ta saka hotunan wasu jarumai a dakin da take hira da mutane amma ba’a ga hoton Adam A. Zango ba.
Magoya bayan Adam A. Zango sun rika kiranta da butulu.
Saidai a dazu ta musu martani a Instagram inda tace mutum da gidansa ya kamata ace zai iya yin fendin da ya ga dama.