
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, ba zata iya bibiyar inda tshageran Dhajin masu nuna kudi da makamai a Tiktok suke ba.
Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi dashi a gidan Rediyo me suna Nigerian Info.
Yace duk wani me amfani da yanar gizo a fadin Najeriya sun san inda yake zasu iya bibiya da zuwa inda yake dan a kamashi.
Yace amma su tshageran Dhajin suna amfani da manhajar yanar gizo ta Starlink ce wadda gwamnati bata iya bibiyarta shiyasa.