
Kakakin ‘yansandan Jihar Kebbi, Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayar da cikakken bayanin abinda ya faru a masallacin Hotoro.
Yace wanine ya je ya Kashe Ladani
Yace wanda ake zargin an samu makogoron Ladanin a aljihunsa.
Kuma da suka je sun tarar da gawarwakin mutanen biyu bayan da jama’a suka farwa wanda ake zargin shima suka aikashi Lahira.
Yace an kai gawarwakin nasu zuwa Asibiti, inda Likitoci suka tabbatar sun mutu
Yace suna kan Bincike kuma suna fatan mutane zasu basu hadin kai.