
Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, babu gudu ba ja da baya ta shirya tsaf dan ci gaba da zanga-zangar data shirya ayau.
Hakan na zuwane bayan ganawar da kungiyar ta yi da shugaba Tinubu a daren ranar Talata.
Shuganan NLC, Joe Ajaero ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar NLC cewa zasu fita zanga-zangar da suka shirya yau ba fashi.
Tuni hukumar ‘yansandan Najeriya ta sanar da kai jami’an ta na musamman gurare daban-daban dan hana bata gari shiga zanga-zangar su batata.