Tuesday, May 19
Shadow

Ba gudu ba ja da baya sai mun yi zàngà-zàngàr da muka shirya>>Inji Kungiyar Kwadago bayan ganawa da shugaba Tinubu

Kungiyar Kwadago ta NLC ta bayyana cewa, babu gudu ba ja da baya ta shirya tsaf dan ci gaba da zanga-zangar data shirya ayau.

Hakan na zuwane bayan ganawar da kungiyar ta yi da shugaba Tinubu a daren ranar Talata.

Shuganan NLC, Joe Ajaero ya bayyana wa manema labarai a hedikwatar NLC cewa zasu fita zanga-zangar da suka shirya yau ba fashi.

Tuni hukumar ‘yansandan Najeriya ta sanar da kai jami’an ta na musamman gurare daban-daban dan hana bata gari shiga zanga-zangar su batata.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon:Munji Dadin Abinda Kwamitin Shura na Kano suka yi game da Malam Lawal Triumph, Yanzu muna jiransu su kira wadanda suka cewa Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Raqumi da Hankaka suma su kawo hujja a litattafan da suka samo hakan>>Inji Shugaban Izala, Sheikh Bala Lau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *