
Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, hukumar birnin ta fara karbar haraji daga hannun masu amfani da janareta saboda damun mutane da kararsa ke yi.
Hakan na zuwane mutane ke kukan rashun wutar Lantarki da kuma matsin rayuwa da suka fada cikin.
An ga takardar karbar irin wannan haraji na ta yawo a kafafen sada zumunta inda da yawa ke ta mamaki.