
Dan takarar shugaban kasa, na jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, ya je wasu makarantun Allo inda ya tambayi nawa ake biyan malaman?
Yace Ya yiwa malaman Albashin Naira 50,000.
Sannan kuma ya dauki malaman koyar da Turanci da Lissafi da kimiyya da fasaha suma ya musu Albashin Naira dubu 50,000.
Ya bayyana cewa, yana da yakinin yaran zasu sama masu amfani anan gaba.