Wednesday, December 24
Shadow

Kalli Bidiyon: Malamin Addinin Islama, Bayerabe, Ahlussunah yace Bikin Eyo Festival na Al’adun Yarbawa da shugaba Tinubu ya halarta shirkane

Wani malamin addinin Islama Bayerabe, Ahlussunah me suna Shaykh AbdulHakīm AbdurRaheem Al Kutubi ya bayyana cewa Bikin Eyo Festival na al’adun Yarbawa da shugaba Tinubu da matarsa Remi suka halarta shirkane.

Malamin yace musulmi bai kamata ya halacci wannan bikin ba.

Shugaba Tinubu bayan ya je Legas inda yake hutun Kirsimeti acan an ganshi a wajan Bikin Eyo Festival inda aka ganshi suna rawa shi da matarsa Remi.

Karanta Wannan  Hotuna: 'Yansandan Najeriya sun fara aiki da motar zamani

Hutudole ya fahimci cewa, wannan bikin ana yinshi ne dan girmama wasu manyan mutane a kabilar yarbawa da suka mutu wanda har bauta musu ana yi, da kuma girmama masu sarautun gargajiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *