
An ga Tauraron fina-finan Hausa, Tijjani Asase cikin hawaye yana jimamin Rasuwar Tauraruwar jarumar Fim din Labarina, Fulani.
Yayi kira ga abokan aikinsa ‘yan Fim da cewa su rika tuna mutuwa su rika kallon wadanda suka rasu sannan su yi hattara da irin abinda suke shukawa.