
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya je jihar Benue inda yake wakiltar shugaban kasar wajan daurin auren dan sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume.
Za’a daura aurenne tsakanin Samuel Aondoakura da Deborah Ershim.
Sakataren Gwamnatin tarayyar, George Akume da Gwamnan jihar Benue, Dr. Hyacinth Alia da sauransu ne suka tarbi shugaban kasar.
Sanarwar ta fito ne daga bakin me magana da yawun mataimakin shugaban kasar, Stanley Nkwocha.
Hakan na zuwane kasa da sati daya bayan da shima sakataren Gwamnatin Tarayyar, George Akume ya auri matarnan me yawan auren manyan mutane watau Zainab wadda ta tabata auren gwamna, Sanata, Basaraken Yarbawa da Wani Balarabe dan gidan sarauta.